Connect with us

Siyasa

2023: Kotu ta tabatar da Uba Sani a matsayin Dan takarar kujerar Gwamna Kaduna a jami’ar APC

Baban kotun taraya dake jihar Kaduna ta tabatar da Sanata Uba Sani, a matsayin Dan takarar gwamna na jami’ar APC a Kaduna.

Mai sharia Mohammad, na baban kotun taraya dake kaduna shi ya zartar da hukunci a ranar juma’a a Kaduna.

A ranar 20 ga watan yuni, 2022 ne abokin takarar Sanata Uba Sani, Hon. Sani Sha’aban, ya shigar da karar, in da ya bukaci kotu ta soke zaben fidda gwani da ya ba Uba Sani, nasara zama dan takara Gwamna a jami’ar APC.

Sha’aban ya soki cewa an gudanar da zaben fidda gwani ba bisa ka’ida ba da kuma delagates.

A ranar 24 ga watan mayu, 2022 ne jami’ar APC ta gudanar da zaben fidda gwani na yan takarar kujerar gwamna a jihar Kaduna, inda Uba Sani yayi nasara da kuri’u 1,149.

A WANI LABARI: Kakakin majalisa jihar Kaduna ya samu lambar yabo gwarzon jagoran siyasa ta shekarar 2022

Kakakin Majalisar Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani, yasamu lamban yabon gwarzon jagaran siyasa ta Leadership Excellence Awards 2022.

Andai karamar kakakin ne a gun taro da ya gudana a Transcorp Hilton Hotel, dake baban birnin taraya Abuja.

Inda yasamu  rakiyar mataimakin kakakin majalisar, shugaban marasa rinjaye, da sauran masu girma ‘yan majalisar dokokin jihar Kaduna da shugabannin zartaswa na karamar hukumar Kaduna.

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.