Connect with us

LABARAI

Farfesa Ashafa ya mika ragamar jami’ar Kaduna ga sabon VC Farfesa Abdullahi

Farfesa Abdullahi Ashafa, shugaban jami’ar Kaduna (KASU), na rikon kwarya ya mika ragamar jami’ar ga sabon shugaban jami’ar Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, wanda shine zai jagoracin ragamar jami’ar.

An gudanar da bikin mika ragamar ne a jiya litini a cikin jami’ar dake birnin Kaduna.

Tun bayan karewar wadin Farfesa Tanko bisa jagoracin jami’ar, gwamnati Kaduna ta mince da miki ragamar jami’ar ga Farfesa Yohana Tella, na rikon kwarya inda daga bisani aka bai wa Farfesa Ashafa.

A wani labarin kuwa: Uba Sani ya karbi ‘yan PDP 12,800 da suka sauya sheka zuwa APC a karamar hukumar Giwa

Farfesa Ashafa, ya karbi jagoracin ragamar jami’ar Kaduna a ranar 23 ga watan yuni zuwa 14 ga watan nuwamba 2022.

Duk da karancin lokaci da yayi Farfesa Ashafa ya taka rawar gani sosai musaman kan batun yajin aiki da yatarar malaman jami’ar keyi.

A ranar 19 ga watan oktoba ne gwamnatin Kaduna ta fitar da sanarwa zabin Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, a cikin jerin mutum biyar da aka kaiwa Gwamna Elrufai a matsayin wanda suka chanchanta.

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.