Connect with us

LABARAI

Gwamna El-Rufai ya yi afuwa ga fursunoni hudu a Kaduna

Gwamna Nasir El-Rufai ya yi afuwa ga fursunoni 4 domin tunawa da cikar Najeriya shekaru 62 da samun ‘yancin kai.

Wadanda aka yi wa afuwar sun hada da Abdullahi Haruna, Usman Ahmed, Mohammed Sani da Khalillullahi Mohammed.

Wata sanarwa daga gidan Kashim Ibrahim ya fitar ta bayyana cewa sakin fursunonin wata al’ada ce ta tausayi da Gwamna El-Rufai ya nuna, bisa ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ya ba shi. Gwamnan ya yi aiki ne bisa shawarar majalisar bada shawara ta jihar kan haƙƙin jinƙai.

Wadanda aka yi wa afuwar sun shafe shekaru uku zuwa sama, kuma suna da watanni shida ko kasa da haka zuwa karshen zaman gidan yari. Gwamna El-Rufai ya bukaci fursunonin da aka yi wa afuwa da su kasance masu halin kirki yayin da suke haduwa da iyalansu tare da kara cudanya da su cikin al’umma.

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.