Connect with us

LABARAI

Gwamnati Kaduna ta nada sabbin sarakunan gargajiya guda uku

Gwamna Elrufai ya amince da nadin sabin sarakunan gargajiya guda uku, sarkin Jere, Kachia da Kufana.

Bayanin hakan na kunshe a wata sanarwa da mai kula da sha’anin watsa labarai na gwamnati Kaduna Muyewa Adekeye, ya fitar a ranar juma’a a Kaduna.

Nadin yabiyo bayan cika dukan sharuda da tsarin nadin sarakunan mai lamba 21 na shekara 2021 ta bayana ( Kaduna State Traditional Institution Law No 21 of 2021).

Sanarwa ta bayana cewa,”biyo bayan shawara daga ministiri kanana hukumomi, gwamnati Kaduna ta amince da nadin:

1. Alhaji Abdullahi Daniya Jere, sarkin Jere, karamar hukumar Kagarko

2. Mr. Zamani Dogonyaro, Agom Kachia, karamar hukumar Kachia

3. Mr. Titus Dauda, Agom Kufana, karamar hukumar Kajuru.”

A wani labarin kuwa: Kotu ta tabatar da Uba Sani a matsayin Dan takarar kujerar Gwamna Kaduna a jami’ar APC

Baban kotun taraya dake jihar Kaduna ta tabatar da Sanata Uba Sani, a matsayin Dan takarar gwamna na jami’ar APC a Kaduna.

Mai sharia Mohammad, na baban kotun taraya dake kaduna shi ya zartar da hukunci a ranar juma’a a Kaduna.

A ranar 20 ga watan yuni, 2022 ne abokin takarar Sanata Uba Sani, Hon. Sani Sha’aban, ya shigar da karar, in da ya bukaci kotu ta soke zaben fidda gwani da ya ba Uba Sani, nasara zama dan takara Gwamna a jami’ar APC.

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.