Connect with us

Siyasa

2023: Isah Ashiru Kudan ya kadamar da kungiyar magoya baya na Tafiyar Amana 2023

Dan takarar gwamna jihar Kaduna a karkashin jami’ar PDP, Hon. Isah Ashiru Kudan, ya kadamar da wata kungiyar magoya baya me suna “Tafiyar Amana 2023” don tabatar da nasara jam’iyar PDP tayi nasara a zabe mai zuwa.

A yayin jawabin sa a ranar talata, gun bikin kadamar da kungiyar magoya bayan Tafiyar Amana 2023, Kudan ya bayana cewa a yanzu haka a maida ana kalon siyasa a matsayin abin kyama.

A Wani labarin kuwa: Kungiyar dalibai Arewacin Nijeriya sun baiwa shugaban hukumar bayar da agajin gagawa na jihar Kaduna lambar yabo

A cewarsa: “Da mutanen da suka dace a fagen siyasa, za a yi abin da ya dace kuma batun duk wani bacin rai ga kowa ba zai taso ba. Al’ummar jihar baki daya za su hada kai domin ganin sun bi abin da ke gabansu a matsayin iyali.”

Ya godewa wada ta samar da kungiyar na goyon bayan Misis Esther Abba bisa wannan shiri da kuma burin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben badi, ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar a jihar da su tabbatar da cewa ba za a bar kowa ba har sai jam’iyyar ta karbi mulki. shugabancin jihar.

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.