Connect with us

Illimi

Jami’ar Kaduna ta bude shafin neman gurbin karatu kakar 2022/2023

Jami’ar jihar Kaduna (KASU) ta sanar da bude shafin neman gurbin karatu digiri farko da diploma na kakar shekara 2022/2023.

Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa da tafito daga ofishin Rijistaran jami’ar, Samuel Manshop.

Inda sanarwa ta kara da bayana cewa jami’ar ta amince da maki 160 a mafi karanci maki a JAMB, ga masu sha’awar karatu a jami’ar.

Shafin an bude cike fom din zai kwashi kwana talatin kafin a rufe shi, tundaga ranar 1 zuwa 30 ga watan nuwamba 2022.

Dole ne sai dalibai sun sanya jami’ar Kaduna a matsayin zabin farko sanan suna da kiredit 5 ciki harda darasin turanci da lisafi a jarabawa WAEC, NECO, NBAIS da NABTEB.

Dalibai su garzaya shafin cike fom din jami’ar me adireshin Yanargizo www.fomrs.kasu.edu.ng, domin cike fom din.

Sanan dalibai zasu biya naira dubu biyu kacal kudin fom din.

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.