Connect with us

Illimi

Jami’ar KASU ta dage cigaba da karatu kakar 2021/2022 sai watan Janairu 2023

Jami’ar Kaduna (KASU), ta dage batun cigaba da karatu kakar 2021/2022 da aka fara har sai zuwa watan Janairu 2023.

Bayanin hakan na kunshe a cikin wani sanarwa dauke da sa hanun shugaban sashin tsarin karatu na Jami’ar, Dr S. M Tahir a ranar 3 ga watan nuwamba 2022.

Sanarwa ta bayana cewa, ” Biyo bayan shawaran hada gurbin karatu shekarar 2021/2022 da na shekara 2022/2023 da kuma duba da haryanzu akwai wanda basu gama rubuta jarabawa ba na zangon karatun 2020/2021.

A don haka Ina sanar muku da cewa Senate din jami’ar sun amince da sake fasalin Kalandar karatu zangon 2021/2022.

Dukan tsangayoyin da basu gama jarabawa ba za su cigaba da gudanar da jarabawa su.

Har ila yau, an dakatar da karatun zango 2021/2022 da yafara gudana, za a dawo cigaba da rijistan da tantance sabi da tsofi dalibai daga ranar 5 zuwa 21 ga watan Disamba, 2022 yayin da za afara gudanar da karatu daga ranar 9 ga watan Janairu, 2023.” .

Zuwa lokacin wanan sanarwa, a na cikin mako na biyu na fara gabatar da karatu kamar yadda tsohuwar kalandar 2021/2022 ta bayana.

A WANI LABARIN JAMI’AR KADUNA (KASU) TA FARA SAIDA FORM DIN GURBIN KARATUN KAKAR SHEKARA 2022/2023

Jami’ar Kaduna ta bude shafin ta na fom din post UTME da DE na shekara 2022/2023.

Inda ake sa ran rufe shafin daga ranar 30 ga watan nuwamba 2022, shafin zai kasance a Bude tun daga ranar 1 ga watan nuwamba.

Dalibai za su ziyarci shafin a adreshin yanargizo www.forms.kasu.edu.ng, inda zasu biya naira dubu biyu kacal kudin fom din.

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.