Connect with us

Siyasa

Kakakin Majalisar Jihar Kaduna ya samu lambar yabo gwarzon jagaran siyasa ta shekarar 2022

Kakakin Majalisar Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani, yasamu lamban yabon gwarzon jagaran siyasa ta Leadership Excellence Awards 2022.

Andai karamar kakakin ne a gun taro da ya gudana a Transcorp Hilton Hotel, dake baban birnin taraya Abuja.

Inda yasamu  rakiyar mataimakin kakakin majalisar, shugaban marasa rinjaye, da sauran masu girma ‘yan majalisar dokokin jihar Kaduna da shugabannin zartaswa na karamar hukumar Kaduna.

Kakakin, ya kara da yin hamdala tare da godiya ga Allah madaukakin sarki, kan wanan lambar yabo da yasamu.

A wani labarin kuwa: Jami’ar Kaduna ta dage cigaba da karatun zango kakar 2021/2022 zuwa watan Janairu.

Jami’ar Kaduna (KASU), ta dage batun cigaba da karatu kakar 2021/2022 da aka fara har sai zuwa watan Janairu 2023.

Bayanin hakan na kunshe a cikin wani sanarwa dauke da sa hanun shugaban sashin tsarin karatu na Jami’ar, Dr S. M Tahir a ranar 3 ga watan nuwamba 2022.

Sanarwa ta bayana cewa, ” Biyo bayan shawaran hada gurbin karatu shekarar 2021/2022 da na shekara 2022/2023 da kuma duba da haryanzu akwai wanda basu gama rubuta jarabawa ba na zangon karatun 2020/2021.

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.