Connect with us

LABARAI

KDSG ta tura Malamai 2000 a Makarantu domin inganta Ilimin Yara mata

Gwamnatin jihar Kaduna ta tura malamai 2000 a makarantu jihar a wani mataki na magance matsalolin ilimin yara mata a jihar.

Mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ta bayana hakan a lokacin da take jawabi a wajen wani horo da kungiyar ‘yan mata masu tasowa ta AGILE a karkashin ma’aikatar ilimi tare da hadin gwiwar hukumar kula da ayyukan malamai a jami’ar jihar Kaduna (KASU) ta shirya a Kaduna.

Wanan yunƙurin yana da nufin tabbatar da cewa an ba wa yara mata duk wata dama don cimma cikakkiyar damarmaki su.

Malamai dubu biyu an raba su ne a tsakani makarantu 155 dake fadin kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.