Connect with us

LABARAI

Kungiyar daliban Arewacin Nijeriya sun baiwa shugaban hukumar bayar da agajin gagawa na jihar Kaduna lambar yabo

Kungiyar dalibai Arewacin Nijeriya (NANNS), ta karama shugaban hukumar bada agajin gagawa na jihar Kaduna, Muhammed Mu’azu Mukaddas lamabar yabo na (Icon of Humanitarian), bisa la’akari da ayukan jinkai da yake gudanar wa a jihar Kaduna.

Kungiyar karkashin jagoracin kwamured Abdulrahman Ibrahim sun samu tarba daga mahukuntan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna a jiya.

Kungiyar ta kunshi dalibai daga jami’o’i daban-daban da kuma kwalejojin kimiyyar kere-kere da ke aiki a karkashin inuwar ta.

Sun zo Kaduna ne domin karrama sakataren zartarwa Muhammed Mu’azu Mukaddas a matsayin “babban aikin jin kai” bisa la’akari da ayyukan jin kai da ya yi a jihar.

A wani labarin kuwa: Mataimakiyar gwamna jihar Kaduna ta karbi ba kuncin sabon VC jami’ar Kaduna

Mataimakiyar gwamna jihar Kaduna, Dr Hadiza Balerabe Sabuwa, ta karbi ba kuncin sabon shugaban jami’ar Kaduna Farfesa Abdullahi I Musa.

Ziyara na zuwa ne Jim kadan bayan mika masa ragamar jami’ar da Farfesa Ashafa yayi a ranar litini.

Sabon shugaban jami’ar, ya ziyarci gidan gwamnati Kaduna a ranar laraba inda mataimakiyar gwamna jihar ta tarbe su.

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.