Connect with us

LABARAI

Mataimakiyar gwamna jihar Kaduna ta karbi ba kuncin sabon VC jami’ar Kaduna

Mataimakiyar gwamna jihar Kaduna, Dr Hadiza Balarabe Sabuwa, ta karbi ba kuncin sabon shugaban jami’ar Kaduna Farfesa Abdullahi I Musa.

Ziyara na zuwa ne Jim kadan bayan mika masa ragamar jami’ar da Farfesa Ashafa yayi a ranar litini.

Sabon shugaban jami’ar, ya ziyarci gidan gwamnati Kaduna a ranar laraba inda mataimakiyar gwamna jihar ta tarbe su.

Sabon mataimakin shugaban ya samu rakiyar shugaban hukumar gudanarwar jami’ar KASU, Hussaini Adamu Dikko, magatakarda Samuel Swanta Manshop da kuma mukaddashin Bursar Hauwa Dalhat.

A wani labarin: Farfesa Ashafa ya mika ragamar jami’ar Kaduna ga sabon VC Farfesa Abdullahi

Farfesa Abdullahi Ashafa, shugaban jami’ar Kaduna (KASU), na rikon kwarya ya mika ragamar jami’ar ga sabon shugaban jami’ar Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, wanda shine zai jagoracin ragamar jami’ar.

An gudanar da bikin mika ragamar ne a jiya litini a cikin jami’ar dake birnin Kaduna.

Tun bayan karewar wadin Farfesa Tanko bisa jagoracin jami’ar, gwamnati Kaduna ta mince da miki ragamar jami’ar ga Farfesa Yohana Tella, na rikon kwarya inda daga bisani aka bai wa Farfesa Ashafa.

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.