Connect with us

Illimi

NUBAPOLY ta fara saida fom din gurbin karatu na shekara 2022/2023

Makarantar kimiya da fasaha ta Nuhu Bamali Polytechnic dake Zaria, ta bude shafin ta na yanargizo domin dalibai da ke neman guraben karatu na shekara 2022/2023.

Daliban dake sha’awar karatu a makaranta zasu iya ziyartan shafin makaranta na yanargizo akan adreshin www.nubapoly.edu.ng.

Daliban da suke neman gurbin karatu a bangaren National Diploma zasu danan alamar “POST UTME” a shafin yayin da dalibai dake neman gurbin a Higher Notional Diploma zasu danna alamar “START APPLICATION”.

Fom din kyauta ne ga dalibai masu neman gurbin HND, yayin da dalibai masu neman gurbin ND zasu biya naira dubu biyu (#2000).

Kawo yanzu makaranta bata fitar da ranar da zata rufe saida fom din guraben karatu na shekara 2022/2023 ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.