Connect with us

Siyasa

2023: Uba Sani ya karbi ‘yan PDP 12,800 da suka sauya sheka zuwa APC a karamar hukumar Giwa

Sanata Kaduna ta tsakiya kuma dan takarar gwamna jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya karbi ‘yan PDP da adadin su yakai 12,800 da suka dawo jami’ar APC a karamar hukumar Giwa.

Sanata ya bayana hakan ne a wani walafi da yafitar a shafin sa a Facebook a ranar lahadi.

Uba Sani ya bayana cewa, “A yayin da muke shirin zafafa yakin neman zabe gabanin zaben 2023, na samu damar karbar sama da ‘yan jam’iyyar PDP 12,800 da suka sauya sheka daga karamar hukumar Giwa zuwa babbar jam’iyyar mu ta APC wadda ta kawo karshen PDP a karamar hukumar.”

A wani labarin kuwa: Gwamnati Kaduna ta nada sabbin sarakunan guda uku

An gudanar da taron karban masu sauyin sheka ne a gaban masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a matakin Jiha da karamar hukumar a karkashin jagorancin Shugaban na Jiha, Air Cmdr. Emmanuel Jekada (Rtd).

Wannan gagarumin sauya sheka mataki ne da ya dace ga wadanda suka sauya sheka, kuma babbar fa’ida ce ga jam’iyyarmu, sannan kuma hakan ya nuna karara cewa jam’iyyar adawa gaba daya babu ita a karamar hukumar Giwa. a cewar Uba Sani.

Ya kuma kara da cewa, “‘Yan jam’iyyar adawa a dubbansu sun bayyana sha’awarsu ta shiga babbar jam’iyyar mu, kuma za mu zagaya sauran kananan hukumomi 22 domin tarbarsu, wanda zai kashe jam’iyyar PDP a jihar Kaduna.

Na gode musu saboda ganin ya zama dole su shiga cikin iyali masu son ci gaba da kuma yadda suke son shiga cikin tsarin don ganin cewa abubuwan ci gaba na wannan gwamnati karkashin jagorancin Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ya ci gaba har zuwa 2023.

Ina godiya ga daukacin masu ruwa da tsaki na jam’iyya a matakin jiha da kananan hukumomi da kuma unguwanni, ina kuma kira gare su da su ci gaba da ba da himma domin samun nasarar babbar jam’iyyarmu a dukkan mukamai da za a yi a jiha da tarayya a shekarar 2023.”

Jim kadan bayan kammala taron, Sanata ya jagoranci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da kuma ’yan takara zuwa ga Hakimin Giwa, Alhaji Abdulkarim Aminu, Wamban Zazzau.

Copyright © 2022 Alright Reserve Kaduna Reporters.